Rahotanni

Boko Haram Sun Kwace Karamar Hukumar Kukawa Ta Jihar Borno.

Spread the love

‘yan ta’addan Boko Haram sun kwace karamar hukumar Kukawa ta jihar Borno, inda suka kashe fararen hula da dama wadanda suka koma kauyen a makon da ya gabata.

Majiyoyi daga sojoji sun fadawa SaharaReporters. A ‘yan makonnin da suka gabata sojojin na Najeriya sun yi ikirarin cewa sun fara aikin sharen fage a cikin garin Baga da Kukawa a Arewacin Borno da nufin ba da kyakkyawan yanayin tsaro ga mazaunan da suka dawo.

SaharaReporters sun tattaro cewa maharan bayan kwace garin sun kuma kafa tutar su a cikin garin.

Wani mazaunin Kukawa, wanda ya zanta da sahara yace bada Wanda idonmu ya gani wasu da dama sun mutu, wasu sun sami munanan raunuka.

Ya kuma ce ‘yan ta’addan sun sake kwace garin Kukuwa, duk da sojoji sunyi sanarwar cewa garin ya tsira lafiya a ‘yan makonnin da suka gabata.

Mazaunin yace me yasa sojojin ba su da shirin kare fararen hula A Kukawa kuma alhali sune suka bar su suka koma gidajensu? ”In ji mazaunin. {Kungiyar ta Boko Haram ta fi zama abin tashin hankali a cikin ‘yan lokutan nan, kodayake gwamnatin da ke yanzu ta ce sau da yawa an lalata lagon Kungiyar, kawo yanzu ta kashe mutane sama da 1,500,000 a Arewacin Najeriya tun lokacin da aka fara wannan tawayen a shekarar 2009.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button