Labarai
Boko Haram sun Sace mutun 35 a Hanyar damaturu Zuwa Maiduguri.
Rahotannin sun bayyana cewa yan ta’addan sun kaiwa dogon ayarin matafiya a kusa da Garin Kuturu a garin Jakana, kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a ranar Juma’a da misalin karfe 17:00 na dare.
Maharan sun kashe wata mata a cikin motar Borno Express, wadanda suka kona akalla motoci bakwai a wurin da aka kai harin.
Bayanai sun ce maharan, wadanda suka bayyana a cikin kakin soji, sun sanya shingen kan hanya a kan babbar hanyar da motocin Hilux guda biyar kafin su sace fasinjojin.
Rahotan Hutu dole