Boko Haram ta faro ne daga Zanga Zanga~Gwamna Zullum
Makonni bayan matasa a duk fadin kasar sun fito zanga-zangar nuna adawa da irin ta’asar da jami’an ‘yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami (SARS), Farfesa Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya yinda yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, ya yi gargadi game da zanga-zangar #EndSARS da ta rikide ta zama bala’i. Zulum ya ci gaba da magana a fadar shugaban kasa ta Aso Rock da ke Abuja, inda ya ce rikicin Boko Haram da ya yi fice a yankin arewacin Najeriya ya fara ne da zanga-zangar da matasa a Maiduguri suka yi game da amfani da hular kwano.
Ya ce: “Game da batun #EndSARS, Ina kira ga dukkan’ yan Najeriya, musamman matasa da su yi hankali sosai. Dukkanin labaran na Boko Haram sun faro ne sakamakon zanga-zangar da wasu matasan garin Maiduguri suka yi game da amfani da hular kwano da masu tuka babura ke yi. Kun ga halin da ake ciki yanzu, ”in ji shi. Gwamnan na Borno ya yi gargadin masu yada zanga-zangar #ndSARS. Majiyarmu ta shafinsa na Twitter
Yayinda yake kira ga matasan Najeriya da suyi taka tsan-tsan, gwamnan Borno ya ce dole ne gwamnatinsa ta sake tsugunar da mutane sama da 100,000 da suka rasa muhallinsu zuwa gidajensu. Ya kuma bayyana cewa domin fatattakar masu tayar da kayar baya kasar za ta bukaci fiye da yadda sojoji ke tunkarar ‘yan ta’addan Gwamnan ya bayyana cewa za a bukaci hanyar siyasa don magance Boko Haram Ya yi kira da a samar da ayyukan yi ga matasa da kuma samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasa su koma gidajensu don ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullun.