
Kungiyar Boko Haram ta saki wani sabon Bidiyo, wanda ta nuna wani Soja daya da Dan Sanda daya wadan takamasu a Maiduguri.
Da farko dai Dan sandan mai suna Yohanna James ya ce mayakan Boko Haram din sun kamashi ne a tsakanin Mngunu da Maiduguri.
Shima Sojan mai suna Emmanuel Oscar yace dakarun Boko Haram din sun kamashi ne tsakanin Maiduguri da Mngunu.
Daga bisani ne kuma mayakan na Boko Haram suka harbe wadannan jami’an tsaron na Najeriya.