Labarai

Bola Tinubu zai zama Shugaban Kasa na Uku da Kotu zata tsige a tarihin Africa ~Cewar Atiku.

Spread the love

Biyo bayan zargin tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan, kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar ta bayyana cewa Najeriya ce za ta zama kasa ta gaba a Afirka da za a soke zaben shugaban kasa da ya kai ga zaben dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Bola Tinubu. a matsayin zababben shugaban kasa.

Ku tuna cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben duk da zanga-zangar da jam’iyyun adawa suka yi, wadanda tun daga lokacin suka garzaya kotu domin kalubalantar sakamakon.

Rashin isar da sakamakon zabe ta hanyar na’ura Mai lantarki daga rumfunan zabe 176,606 da INEC ta yi zuwa dandalin jama’a, kamar yadda ka’idojin hukumar suka bukata, na daya daga cikin dalilan da suka janyo cece-kuce daga jam’iyyun da suka sha kaye.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Daniel Bwala, mai magana da yawun yakin neman zaben Atiku, ya bayyana kwarin guiwar cewa za a soke zaben shugaban kasar Najeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 saboda zargin magudin zabe.

Ya ci gaba da cewa Najeriya bayan Kenya da Mali za ta kasance kasa ta uku a Afirka da za’a soke zaben shugaban kasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button