Bom ya kashe Sojojin Nageriya uku 3 a Jihar Borno
Akalla, sojoji uku sun mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka lokacin da ayarin sojojin ya ci karo da nakiya da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka binne a kan hanyar Maiduguri / Gomboru Ngala a ranar Litinin, a cewar majiya.
An gano cewa ayarin wasu bataliyoyi uku na Sojojin Najeriya, wadanda ke rakiyar matafiya, sun yi karo da na’urorin fashewar abubuwa (IEDs) tsakanin Gomboru Ngala da Dikwa
A cewar wata majiya, wanda ya nemi a sakaya sunansa: “Motar da suke aiki [sojoji] ta lalace kuma mun rasa wasu sojoji a Harin na Bama-baman da aka binne a kan hanyar Dikwa / Gomboru Ngala.
Addu’armu da tunaninmu suna tare da iyalansu, ”in ji majiyar.
Har ila yau, wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa mutane uku sun sadaukar da rayukansu”, inda ta kara da cewa motocinsu sun yi mummunan lalacewa fiye da gyara.
“Abin bakin ciki ne, mun rasa sojoji uku a cikin nakiya.
“Sun mutu a kan hanyarsu ta zuwa Gamboru Ngala sakamakon Bama-baman da aka dasa a wani mummunan yanki na hanyar da’ yan ta’addan Boko Haram suka yi a ranar Litinin, ”in ji majiyar tsaron.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, sojoji har yanzu ba su fitar da sanarwa game da lamarin ba. Rahotan Daily trust