Labarai

Borno: Zulum ya kayar da Jajari na PDP ya ci zabe

Spread the love

An ayyana Babagana Zulum, gwamnan Borno a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka yi ranar Asabar.

Jude Rabo, jami’in zaben da ke bayyana sakamakon zaben, ya ce Zulum na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu kuri’u 545, 542 inda ya doke abokin takararsa Mohammed Jajari na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 82,147.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Zulum ya doke wasu mutane 11 da suka fafata a gasar.

Haka kuma, kujeru 28 na ‘yan majalisu 28 a jihar APC ta samu nasara, inda Abdulkarim Lawan, shugaban majalisar mai ci, wanda shi ne shugaban majalisar da ya fi dadewa ya lashe zaben a karo na biyar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button