BUA Ta Baiwa Gwamnatin Adamawa Tallafin Covi-19…
Kamfanin BUA Karkashin Shugaban Kamfanin Mal. Abdussamad Isiyaka Rabiu ta Tallafawa Gwamnatin Adamawa da Zunzurutun Kudi Naira Miliyan Dari Biyu 200m da Motocin Daukar Marasa lafiya Guda Uku.
BUA Ta Danka wannan Tallafin Ne a Hannun Gwamnan Jahar Ahmadu Umar Fintiri Jiya Talata a Gidan Gwamnatin Jahar dake Yola.
Tun a Ranar 3 ga watan Yuli ne dai Kamfanin BUA din tayi alkawarin Bada Wannan Tallafin Sai jiya Talata Alkawarin Ya Cika.
Wanda Ya Mika Tallafin a Madadin Shugaban Kamfanin Kuma Tsohon ministan Kula da Lafiya a Jahar Adamawa Dr. Idi Hong ne ya Mika Gudunmawar ga Gwamnan Jahar a Gidan Gwamnati.
Hong yace BUA GROUP Foundation din a Kalla ta Kashe Kudi Sama da Naira Biliyan Bakwai wajen Tallafawa Gwamnatoci da Kamfanoni da Sauransu a kokarinta na Yaki da Corona Virus a Kasar Nan.
Fintiri da ya karbi tallafin yace Yanzu Haka BUA ta Sanya kudin a Asusun Gwamnati sannan ya Yi godiya ga Kamfanin sannan yayi Alkawarin Gwamnati Zatayi amgani da Tallafin Kudi da Motocin Wajen Cigaba da yakar Cutar Corona Virus A Jahar Inji- Gwamnan.
Ahmed T. Adam Bagas