Tsaro

Bugu Da Kari:’Yan Bindiga sun sake sace Ɗalibai a Katsina.

Spread the love

Rahotanni sun ce an sace wasu dalibai uku daga kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina a ranar Talata. Wani mazaunin Gobirawa, wanda …

Rahotanni sun ce an sace wasu dalibai uku daga kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina a ranar Talata.

Wani mazaunin garin Gobirawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar wa da Jaridar Dailytrust cewa an sace daliban ne bayan rufewa daga Makarantar Sakandaren Community Day da ke Gobirawa.

“Ba makarantar kwana ba ce kuma dukkanin mutanen uku da aka sace daliban maza ne kuma an sace su ne da yammacin yau a kan hanyarsu ta komawa gida bayan rufewa daga makarantar,” in ji majiyar.

Majiyar ta kuma kara da cewa akwai rade-radin cewa gwamnatin jihar ta rufe makarantar sakamakon lamarin.

Kokarin tabbatar da rufe makarantar daga jami’an gwamnati ya ci tura saboda kiran da aka yi wa Kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Lawal Badamasi, ba a amsa ba, yayin da Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar, Sani Danjuma, ya ce bai san faruwar lamarin ba, tunda ya kasance ba ya jihar ya je wani aikin da aka tura shi.

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin ‘yan sanda a Katsina, SP Gambo Isah, ya ce zai tuntubi jami’in’ yan sanda na shiyya ta karamar hukumar Safana don jin gaskiyar labarin.

Rohoton Dailytrust.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button