Buhari da Gwamnatin sa ne suka jawo mutuwar mutun 23 a jihar kogi Inji Yahaya Bello
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya dora alhakin fashewar tankar dakon mai a ranar Laraba Wanda ya faru a layin Felele na hanyar Okene / Lokoja / Abuja Gwamna Bello Yace kan mummunan halin da duk titunan gwamnatin tarayya ke ciki a fadin jihar. Bello ya ce rashin kulawa da titin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi Yasa ake rasa rayukan Al’umma
Akalla mutane 23 ne aka tabbatar da mutuwarsu wasu Kuma da dama suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai a kan hanya a ranar Laraba. Motoci sama da biyar ne suka kone kurmus a hatsarin da ya afku, kuma shaidun gani da ido sun ce wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da daliban kwalejin fasaha ta Kogi. Kwamandan sashen na Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa a Jihar Kogi, Idris Fika, ya ce an ciro gawawwaki akalla 23 daga cikin baraguzan jirgin. Bayan afkuwar lamarin,
Gwamna yahaya Bello ya ziyarci Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, kan bukatar Gwamnatin Najeriya ta gyara hanyar da sauran su a fadin jihar. Mai magana da yawunsa, Onogwu Muhammed, a cikin wata sanarwa ya ce gwamnan ya fada wa Ministan cewa mummunan halin da dukkanin titunan gwamnatin tarayya ke ciki a fadin jihar ya haifar da hadurran da ke faruwa a jihar. Sanarwar ta ce, “Ya ce gwamnatin jihar ta yi matukar kokarin kula da hanyoyin amma saboda yawan zirga-zirgar da ke kan titunan, ganin yadda take a matsayin karamar hukuma, irin wadannan gyare-gyare da gyaran ba su tsaya Bata lokacin a karshe Gwamnan “Ya yi kira ga ministar da ya hanzarta aiki a ci gaba da sake gina hanyoyi a duk fadin jihar don rage afkuwar haddura a kan hanyar. “