Uncategorized

Buhari Kayi Abinda Yan Nigeria Zasu Rika Tunawa Da Kai Bayan Ka Kammala Tainuwarka~Gwamnan Sokota

Ahmed T. Adam Bagas

Gwaman jihar Sokoto Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da za a rika tunawa da shi, ya yi abin da zai sa hukumomin kasar su yi aiki yanda yakamata.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a bukin shekara 40 na kamfanin Silverbirth, in da aka bashi kyautar gwamnan da yafi haskawa a 2019 a jihar Lagos

Tambuwal ya roki Buhari yabar wani abin kwaikwayo ga Na Bayansa da za a rika tunawa da shi don yanzu babu abinda Za’a Ce yayi Na Azo Agani a Kasa.

Tambuwal Yace a Shekarar 2015 Ya Goyi bayan Shugaba Buhari Da Zummar Zai Kawowa Kasar Chanji Mai Kyau, Amma sai Sukaga Akasin Haka Shi yasa Suka Jaa Baya Sukasa Ido Hasalima Sukabar Party Mai Mulki. Inda Yace Ya Shwarci Buhari da Ya yi Abinda Yan Kasar Zasu Yabeshi Ko Bayan ya Kammala Wa’adisa Na Karshe a Shekarar 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button