Buhari Ne Yasa Kayan Abinci Sukai Tsada A Najeriya__Martanin Hon. Sale Shehu Hadejia Ga Gwamnan Jigawa Badaru.
Na kalubalanci jawabin gwamna badaru Na jigawa Wanda yayi bayanin cewa, jam iyar PDP da shugaba Muhammadu Buhari yagada itace ta jawo kayan masarufi sukai tsada a Najeriya kamar yadda gwamnan ya bayyana wasu dalilai wadanda suka hada harda maganar karbar harajin shigo da kaya da sauran su.
Na tabbatar mafi yawan masu shigo da kaya daga kasashen ketare mutanen cikin gida Najeriya ne, sannan tun a wancan lokacin ma mutanen Najeriya Na gudanar da sana’o’in noma ba wai se hawan gwamnatin Buhari suka fara noma ba.
Na tabbatar manoma a wancan lokacin sunfi samun sukuni wajen gudanar da noma idan kayi duba da farashin manfetur baiwuce naira 85 ba.
Sannan takin zamani baiwuce 2500 ba. Banda kuma Wanda gwamnati take rabawa munoma kyauta.
Dalilin dayasa Na kalubalanci jawabin gwamna badaru cewa wai ba Buhari bane yasa kayan abinci sukai tsada a Najeriya ba sune kamar haka:
A matsayin shugaba Buhari Na ministan manfetur Wanda yazo ya tarar da manfetur naira 85, amma ya tayar da farashin manfetur din daga naira 85 zuwa naira 150, shine dalili Na farko Na tsadar kayan masarufi a Najeriya.
Sale Shehu yakara da cewa: tsadar takin zamani a Najeriya, tun zuwan shugaba Buhari takin zamani yabar farashin naira 2500 ya koma zuwa farashin naira 5000, wannan yana daga cikin tashin kayan masarufi a Najeriya.
Hana shigowa da kayan masarufi a Najeriya bayan Najeriya bata wadata mutanen ta da isasshen wajen noma ba, bata bawa mutanen ta tallafi domin noma ba, bata samar da kyawawan kayayyakin sarrafa kayan abinci ba domin mutanen ta, amma ka tsaye ta hana shigo da kayan masarufi daga ketare kawai don ta karbi haraji babu ruwanta da wahalar da mutanen ta zasu shiga.
Idan gwamnati zatayi maganar cewa mutane basa biyan isasshen haraji a wancan lokacin domin shigo da kayan Abinci to shikenan a wannan gwamnatin se ayi mana bayanin wanne abubuwan more rayuwa talakawa suke amfana da kudin harajin da take karba. Musamman mu mutanen Arewacin Najeriya.
Don haka Na kalubalanci jawabin gwamna badaru_ inji Hon. Sale Shehu hadeja.
Daga Kabiru Ado Muhd.