Labarai
Buhari Ya Amince a fitar da dala biliyan, 1.9 Domin Layin Jirgin Kasa daga Kano Zuwa Jamhuriyar Nijar.
Ya ce layin dogo da ake shirin yi daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar zai kai tsawon kilomita 248 kuma zai ratsa gundumomin sanatoci bakwai a Arewa.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da kwangilar Samar da layin dogo daga Kano zuwa Katsina zuwa Jibia zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar da Dutse, babban birnin jihar Jigawa, kan jimlar kudi dala 1,959,744,723.71.
An cimma matsaya ne a taron Majalisar Zartarwar Tarayya a yau Laraba, in ji Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Ya ce layin dogo da ake shirin yi daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar zai kai tsawon titin da zai kai kilomita 248 kuma zai ratsa gundumomin sanatoci bakwai a Arewa.
Ahmed T. Adam Bagas