Buhari ya amince da yin rijistar kyautar 250,000 ga ‘yan kasuwa.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da rijistar sunayen ‘yan kasuwa kananan da matsakaitan kamfanoni (MSMEs) na fadin kasarnan.
Mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad wanda ya bayyana hakan a cikin wani sakon Twitter a ranar Talata, ya ce Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC) ta ba da sunaye 6,606 ga kowane daga cikin jihohi 34, yayin da Abuja za ta kasance da 7,906, Lagos 9,084 da Kano 8,406.
Rijistar, in ji shi, ta fara ne a ranar Talata kuma ana iya yin ta ta hanyar http://cac.gov.ng. “Pres. @MBuhari ya amince da rijistar sunayen kasuwanci kyauta ‘na 250k MSMEs a duk ƙasar; a cewar CAC, sunaye 6,606 a kowacce daga cikin jihohi 34, Abuja zata samu 7,906, Lagos 9,084 & Kano 8,406, ”Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter. “Rijistar kyauta ta fara yau, ziyarci http://cac.gov.ng don cikakkun bayanai.”