Labarai

Buhari ya aminta zai biya Bilyan N4.75bn ga dillalan shanu dana abinci amatsayin diyya.

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta amince za ta biya kungiyar hadahadar kayan abinci da dillalan shanu a Najeriya (AUFCDN) Naira biliyan 4.75

Shugaban kungiyar ta AUFCDN, Muhammad Tahir ne ya bayyana hakan a Abuja bayan wani taro da ya yi da hukumomin gwamnatin tarayya, wanda gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya wakilta.

“Duk masu ruwa da tsaki da mambobin kungiyar AUFCDN a yajin aikinmu na kasa baki daya suna farin cikin cimma nasarar da muke son cimmawa. Tunda Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya roke mu a madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya, mun amince da janye yajin aikin a duk fadin kasar a yau.

“Sun amince su biya diyyar tare da dakatar da biyan haraji da yawa a kan manyan titunan gwamnatin tarayya kuma su ba mu damar shiga harkokin kasuwancinmu cikin lumana a duk fadin kasar,” Mr. Tahir yace.

Mista Tahir ya bayyana wa Nation cewa Aso Villa ta amince da tabbatar da kare membobinta, dakatar da yawan haraji da tsoratar da jami’an tsaro a kan hanyoyi.

Sauran bukatun da Mista Bello ya gabatar a gaban gwamnati ta hannun Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, sun hada da kariyar mambobin kungiyar da kuma damar janye ayyukanta daga jihohi idan har an kai hari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button