Labarai
Buhari Ya Bar Najeriya Zuwa Yamai Nijar..
Buhari ya bar Najeriya Zuwa Yamai A Yau Litinin – 7 ga Satumba, 2020.
Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da rahoto na musamman kan COVID-19 a wajen taron.
Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, 7 ga Satumbar, 2020, don halartar Taron Tattaunawa na 57 na kungiyar ECOWAS.
Malam Garba Shehu, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya sanar da hakan a ranar Lahadi, 6 ga Satumba, 2020, a cikin wata sanarwa a shafin Twitter.
Daga Mujaheed Umar D Giwa.