Buhari Ya Jinjinawa Tambuwal da Sarkin Musulmi.
Shugaban kasa muhammadu buhari ya jin jinawa Gwamnan Jahar Sokoto Rt. Hon. Aminu waziri tambuwal, da Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar 111 bisa Jarir cewar su ta Fannin samar da Tsaro a Jihar Sokoto.
Buhari yayi wannan yabon ne Ranar asabar da Tagabata a wajen Daurin Auren `yar Sarkin Musulmi Hajiya Zainab Fodio a Fadar Mai Alfarma Sa’ad Abubakar a Nan Birnin Shehu.
Wanda yayi Jawabin Hakan a Madadin Shugaban Kasa, Ministan Shara’a Kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya. Abubakar Malami (SAN), Inda Yasamu rakiyar Ministan Kula da Harkokin Yan Sanda da Shugaban Rundunar
Yan Sanda Ta Kasa IG. Abubakar Adamu.
Malami yace Buhari ya godewa Gwamnana Tambuwal da Sultan Na Sokoto, Kan yadda suke Aiki Kafada da kafada da gwamnatin Tarayya wajen Samarda Tsaro a Fading Jihar Sokoto dama Kasa Baki daya Inji SAN.
Ahmed T. Adam Bagas