Buhari ya roki Ma’aikatu masu zaman kansu da su dauki matasan Nageriya Aiki.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci bangarori masu zaman kansu a fadin Jihohi 36 na tarayyar da suka hada da babban birnin tarayya, Abuja da su nuna sha’awar daukar matasan Najeriya aiki a cibiyoyin su.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a garin Abakiliki a ranar Litinin lokacin da aka fara bikin kaddamar da shirin fadada ayyuka na musamman (ESPWP) wanda aka gudanar a Abakiliki.
Ya bayyana cewa fara shirin a duk fadin kasar, shi ne burin gwamnatinsa wajen tunkarar abin da ya biyo bayan cutar ta COVID-19 da kuma matsalar #EndSARS.
Ya kara da cewa cutar ta COVID-19 wacce ta addabi duniya baki daya a farkon shekarar da ta gabata, ta haifar da mummunar tabarbarewar tattalin arziki a kasar, yana mai jaddada cewa hakan ya kara ta’azzara yawan rashin aikin yi a kasar.
“A kan wannan bayanin, zan so in yi amfani da wannan damar in yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su nuna sha’awar yin amfani da matasan Najeriya musamman ma wadannan mahalarta bayan sun samu ilimi da dabaru wajen aiwatar da wannan shirin.”
Shugaba Buhari wanda ya bayyana kwarin gwiwa game da makomar tattalin arzikin mahalarta taron, ya lura cewa shirin zai baiwa wasu daga cikinsu damar yin ayyukan dogaro da kai.
Tun da farko, Shugaban kungiyar ta fadada shirin na musamman na ayyukan gwamnatin tarayya, Dokta Edward Nkwegu ya ce gwamnatin tarayya za ta kashe kimanin naira miliyan dari bakwai da tamanin a cikin watanni uku na isar da shirin a jihar kadai.
“Mutum dubu daya da aka dauka aiki a kowace karamar hukuma gwamnatin tarayya za ta dauki nauyin su tsakanin watan Janairu zuwa Maris na wannan shekarar.
“Kuma za a biya su jimillar dubu 20 kowannensu na tsawon watanni uku kuma Ebonyi ta dauki jimlar mutane 13, 000 daga kananan hukumomi 13 da ke jihar”, in ji shi.
Daily trust ta tattaro cewa wadanda aka dauka galibinsu mata ne kuma an basu kayan aiki domin yin tasiri yadda ya kamata wanda ya fara a wannan watan.
Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu ne ya wakilci Shugaban kasar a wajen taron.