Buhari ya sake aminta da karbo bashin Daloli Bilyan $35bn Inji Amaechi
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince Najeriya ta karbi rance. Amaechi ya bayyana hakan ne a lokacin taron murnar cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai a gidan Talabijin na Channels ranar Alhamis.
A cewar tsohon Gwamnan na Jihar Ribas, rancen na nufin samar da ababen more rayuwa a sassa da dama na kasar. “Shugaban kasa (Muhammadu Buhari) ya ba mu damar aro. karbar bashin don bunkasa abubuwa da dama ”inji shi.
Amaechi ya bayyana cewa lokacin da aka siyar da danyen mai a $ 120 kan kowacce ganga, jumullar kudin da ake bukata domin bunkasa layin dogo a fadin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT) ya kasance tsakanin $ 35billion zuwa $ 40billion.
Ba haka ba ne a da. Muna da kuɗi don gina wannan hanyar jirgin ƙasa. Kudaden da muke bukata domin kammala aikin titin jirgin kasa baki daya ya kai dala biliyan $ 36billion zuwa $ 40billion. “Muna da wannan kudin lokacin da muke sayar da danyen mai kan dala 110 zuwa $ 120 kan kowace ganga. Yanzu, kudin ba su nan, ”in ji Amaechi.