Buhari ya yi sallar Juma’ar ta karshe a Aso Rock
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Juma’a, ya yi sallar Juma’a ta karshe a fadar shugaban kasa.
Buhari ya samu rakiyar Bola Tinubu, zababben shugaban kasa.
Bayan kammala Sallar Juma’a, Buhari ya kai Tinubu rangadin zagayawa a sassan da ke aiki a fadar gwamnatin yayin da wa’adin sa ke kawo karshe a ranar 29 ga watan Mayu.
A yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala rangadin, Tinubu ya ce ya yi addu’ar Allah ya ba shi lafiya ya fuskanci kalubalen.
“Ka taimake ni Allah, don ɗaukar nauyi, in fuskanci kalubale, kuma ka kiyaye ni cikin koshin lafiya, in sami damar cika mafarkai da burin miliyoyin mutanenmu,” in ji shi.
A ranar Alhamis, Buhari ya yi wa Tinubu da Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa kambun karramawa.
Daga bisani, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya kai Shettima, magajinsa, ziyarar gani da ido na fadar shugaban kasa.
A kasa ga hotunan ziyarar Buhari da Tinubu.