Siyasa

Buhari Yafi Shugabannin Ku Kuma A Mulkinsa Yayi Maganin Cin Hanci APC Ta Mayarwa Da PDP Martani.

Spread the love

Jam’iyya me mulki ta APC ta mayarwa da jam’iyyar hamayya ta PDP martani akan caccakar da tawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan cewar da yayi zai mayar da hankali kan wasu muhimman ayyuka 9 a shekaru 3 da suka rage masa akan mulki.

A sanarwar data fitar ta hannun sakataren watsa labaranta, Yekini Nabena, APC ta bayyana cewa PDP fa bata da bakin magana. Mun fahimci sanarwar ta bayyana cewa PDP na kara nunawa ‘yan Najeriya dalilin da zai sa ba zasu kara zabarta a matsayin jam’iyyar da zata mulkesu ba.

Yace a zamanin Shugaba Buhari Najeriya ta zama giwar Africa wajan karfin tattalin arziki, ta kuma fara ciyar da kanta abincin da take nomawa, an samu daidaiton farashin man fetur dadai sauransu.

Yace APC da sauran ‘yan Najeriya da suka san abinda suke zasu ci gaba da goyawa gwamnatin shugaban kasa,Muhammadu Buhari baya dan ta kai ga gaci.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button