Labarai

Buhari yana da girman kai da nuna ɗagawa, in ji tsohon shugaban ƙasa Abdussalamu Abubakar.

Spread the love

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya na mulkin Soja janar Abdussalam Abubakar ya bayyana shugaban ƙasa Muhammad Buhari a matsayin mutum mai girman kai da nuna ɗagawa.

Janar Abdussalam Abubakar ya ce girman kai ma rashin daukar shawara daga wajen waɗanda suka san sirrin Najeriya ne yake neman sanya ƙasar ta tarwatse a ƙarkashin mulkin nan na Buhari..

Janaral ɗin ya ƙara da cewa da Buhari zai ajiye girman kai ya gwada aiki da shawarwarin da tsoffin manyan ƙasarnan ke bashi kuma suke ci gaba da bashi, to da babu shakka zai iya maganin wasu abubuwa da suka shige masa duhu koda ba gaba daya ba.

Janar Abdussalam Abubakar ya fadi haka ne yayin da wasu gungun ‘yan jaridu ke ganawa dashi game da halin da Najeriya take ciki yau a ƙasar Ghana bayan idar da sallar juma’a a babban masallacin birnin Accra.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button