Rahotanni
Buhari zai karrama Tinubu da Shettima ranar 25 ga Mayu
A ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai karrama zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da Kashim Shettima, mataimakin shugaban kasa.
Tinubu dai za a ba shi babban kwamandan oda na Tarayyar Najeriya (GCFR) yayin da Shettima za a karrama shi da Grand Commander of the Order of the Niger (GCON).
Tolu Ogunlesi, mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin dijital da sabbin kafafen yada labarai, ya sanar da ci gaban a ranar Alhamis.