Buhari Zai Kashewa jihohin Katsina da Kano da jihohi 7 N110bn Akan Manyan Ayyuka.
A taron FEC a ranar 2 ga Disamba, 2020, an yanke shawarar cewa za a kashe N117.661b wajen gina hanyoyi da gadoji a wasu jihohin.
Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola SAN, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.
Za a kashe N8.7b a kan babbar hanyar Kano-Kazaure-Daura-Mai’adua.
Fashola ya bayyana cewa majalisar FEC ta amince da gyaran wasu hanyoyi da suka hada da Omor-Umulokpa da Oye-Oranto a kan N1.712b da N2.5b.
Har ila yau, a ranar Laraba, Ministocin sun amince da bayar da kwangilar aikin gadar Okpokwu a kan hanyar Ogoja-Okuku-Aliforkpa-Benue da ke Kuros Riba kan N1.06b.
Ministan ya ce aikin titin Bida-Zungeru na N1.02b a jihar Neja ya samu amincewa. Tsakanin jihohin Abia da Enugu, za a gina gadar Nkwumi kan kudi N1.07b.
Gwamnatin Tarayya ta kuma amince da gina hanyar Chalawa-Runku-Sawa-Kayi a Kumbotso, Kano.
Sauran ayyukan da majalisar ta amince da su sun hada da titin Riga-Gusau a Zamfara, titin Jigakwana da titin Kokomo Auta duk a cikin jihar ta Kebbi.
Akwai kuma ayyukan titin kan Kuka Babangida, Ihiala-Orkula-Umuduru, Oye Ama Otite-Umuawulu, da kuma gyaran hanyar Bichi, Ministan ya ce a jiya.
Fashola ya ce FEC ta amince da aiki da software na bankin gidaje, FMB akan kudi N487.394,285.71. Ministan ya bayyana fa’idar wannan software da za’a gani.
Source: Naija News