Rahotanni
Buhari zai tafi Landan domin nadin sarautar Sarki Charles III
A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles III.
Yayin da yake kasar Birtaniya, shugaban zai kuma halarci wani taro na shugabanni da shugabannin gwamnatocin kasashen Commonwealth a ranar Juma’a.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cikakken bayanin tafiyar Buhari a cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar Laraba.