Siyasa

Bukola Saraki Zai Canza Sheka Daga PDP Zuwa APC~Hon. Baba Dan Baba.

Spread the love

Wani jigo a Jam’iyya mai mulki Ta APC yayi ikirarin cewa Tsohon shugaban majalisar dattawan Kasar nan, Sanata Abubakar Bukola saraki Zai Koma Jam’iyyar APC.

Dan Baba yayi wannan Iki rarin ne, Kwanaki kadan bayan komawar Tsohon kakakin majalisar kasar nan Hon. Yakubu Dogara zuwa Jam’iyya mai mulki ta APC.

Dan baba “ya ce nan Bada jimawaba wasu gwamnonin PDP uku zasu koma APC Inji Shi.

Sai dai Jaridar Mikiya ta Tuntubi wani makusancin Saraki ta wayar Tarho, Inda yace wannan Maganar banza ce Kuma shaci fadi ne Irin na Siyasa.

Idan baku mantaba dai Saraki shine Shugaban Yakin Neman zaben Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a Shekarar 2019.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button