Burinmu ba zai Cika ba sai anyima kowa Allurar Rigakafin CoronaVirus a Nageriya ~El Rufa’i.
Gwamna Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i Yace A yau hukumomin mu na lafiya a jiharmu ta kaduna sun fara bayar da allurar rigakafin Covid-19 ga ma’aikatan gaba da kuma manyan dabaru.
Na karbi kashi na farko na rigakafin, tare da Mataimakiyar Gwamna Dokta Hadiza Balarabe da manyan jami’an KDSG. Hakanan sanata Uba Sani da Suleiman Abdu Kwari suma sun dauki alluran rigakafin a matsayin wani bangare na kokarin da muke yi na karfafa gwiwar ‘yan kasar mu da ayi musu rigakafin.
Yayin da aka ci gaba da yin allurar rigakafin, ina kira ga dukkan ‘yan kasarmu da su kasance masu lura da kiyaye ka’idojin rigakafin Covid-19. Shigowar allurar rigakafin cutar a jiharmu ba yana nufin ficewar kwayar cutar ba ne.
Har yanzu muna da jan aiki a gaba don yin allurar rigakafin yawan jama’armu don samar da garkuwar ga Jama’armu…