Lafiya
Cakwakiya: Dalibai 7 Da Suka Je Rubuta Jarabawar WAEC Sun Kamu Da COVID-19 A jihar Gombe.
Rahotanni daga jihar Gombe sun bayyana cewa dalibai 7 da suka je rubuta jarabawar WAEC sun kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Habu Dahiru ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace an wa daliban da suka je rubuta jarabawar Gwaji. Mun tattaro muku cewa sai a jiyane sakamakon gwajin ya fito.
Kwamishinan yace kamuwar daliban da cutar Coronavirus/COVID-19 ba zai sa a hanasu Rubuta jarabawarsu ba. Ya kuma bada tabbacin cewa za’a baiwa daliban kulawar data kamata.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe