CIBIYAR KILLACE MUTANE TA COVID-19 DAKE SANI ABACHA STADIUM.
Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kai ziyarar gani da ido yadda aikin kafa cibiyar killace mutane ta filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata ke wakana, wadda na hadin gwiwa ne tsakanin Gidauniyar Dangote da kuma Gwamnatin jiha kuma tana da gado 509. A yanzu haka dai an kammala hada rumfa daya wadda aka saka mata gado 254 hade da katifa da pillow da zanin gado da kuma akwatin ajiye kayan magani da sauran su. Sannan akwai na’urar sanyaya daki. Ana sa ran zuwa jibi rumfa ta biyu mai kimanin gado 254 ita ma zaa kammala ta tare da kayan cikin ta kamar ta farkon nan. Sannna anyi tanadi na musamman wajen tsaftace muhalli a wajen da yadda zaa kwashe shara da kuma bahaya da fitsari wanda shi kan sa aiki ne na kwararru daga maaikatar muhalli wanda sun tanadar da kwararrun maaikatu guda 50 da zasu kula da wannan bangaren. Haka kuma wannan shara zaa raba ta kashi biyu, daya zaa kaita asibitin kwanar dawaki inda zaa kona ta, sannan sharar bandaki kuma zaa kaita Danbatta inda aka tanadar da wajen da za’a binne ta. Sannan an tanadar da jami’an tsaro da zasu tabbatar da tsaro a wajen dare da rana. Gwamna Ganduje na tare da Mataimakin sa kuma shugaban Kwamitin Covid-19 na jihar Kano wato Dr Nasiru Yusuf Gawuna da kuma Kwamishinonin Lafiya, da na Aiyuka da na Yada Labarai da na Wasanni da Matasa da sauran manyan jami’an Gwamnati. Daga Salihu Tanko Yakasai Special Adviser Media Government House Kano April 6, 2020