Cikakken Bayani: Duk Da Karin Dokar Zaman Gida Da Gwamnatin Tarayya Tayi A Jihar Kano Gwamnantin Kano Ta Bayyana Cewar Za’a Cigaba Da Sallar Juma’a Kuma Za’ayi Sallar Idin Karamar Sallah A Jihar.
Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Daga Miftahu Ahmad Panda
Biyo Bayan Karin Makonni Biyu Da Gwamnatin Tarayya Tayi A Dokar Zaman Gida a Jihar Kano, Gwamnatin Jihar Ta Kano Karkashin Jagorancin Maigirma Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje Tayi Gyara Akan Dokar.
A Jiya Litinin ne Gwamnan Jihar Ta Kano yabayyana Cewar Za’a Cigaba Da Sallar Juma’a Kuma Za’ayi Sallar Idin Karamar Sallah a Jihar, Ta hanyar yin Biyayya Ga Dokar Bada Tazara Tsananin Al’ummar Da zasu Ziyarci Masallatai Domin Gudanar Da Sallolin Biyu.
Ana Sa Ran Gudanar Da Sallar Idin Karamar Sallah ne Dai a Ranar Asabar Ko Lahadi Bayan Kawo Karshen Azumin Watan Ramadan Mai Albarka.
Gwamnatin Jihar Ta Kano Ta Fitar Da Wannan sanarwa ne Dai biyo Bayan Sanar Da Kulle Jihar Ta Kano Na Tsawon Makonni Biyu Da Gwamnatin Tarayya Tayi kamar Yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Yaki Da Cutar Covid - 19 ya sanar.
Anasa Bangaren Mai Magana Da yawun Gwamnan Jihar Ta Kano, Salihu Tanko, a takaitaccen Bayanin Da ya wallafa a Shafin Facebook ya Bayyana Cewar Gwamnatin Ta Kano Ta Dauki Wannan matakinne Biyo Bayan Tattaunawar Da Tayi Da Manyan Malamai Guda 30.
Saidai bai Bayyana Cewar Ko Gwamna Ganduje ya tattauna Da Shugaban Kasa ba Kafin Daukar Matakin Gyara Dokar.
Idan Baku Mantaba Dai Ankwashe Makonni Biyar Kenan Ba’a Gudanar Da Sallar Juma’a ba, a Jihar Ta Kano.