Labarai

Cikakkun Labaran Safiyar Lahadi 17/05/2020CE – 24/0/1441AH.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

An samu karin mutane 176 masu dauke da Coronavirus a Najeriya, jimilla 5,621.

Gwamnatin jihar Kano ta ce a hankali za ta janye dokar hana zirga-zirga a jihar.

Gwamnatin tarayya ta ce rashin zuwa asibiti saboda tsoron Covid-19 ne ga marasa lafiya ya haddasa mace-mace.

Kamfanin NNPC ya bai wa Abuja kyautar asibiti don kula da masu cutar Covid-19.

Jihar Sokoto ta sake sallamar mutum 4 wadanda suka warke daga cutar korona a jihar.

‘Yansanda a jihar Neja sun kashe ‘yan bindiga 9 a karamar hukumar Rafi da ke jihar.

Jam’iyyar PDP ta dakatar Sanata Sulaiman Hukunyi da wasu 4 daga jam’iyyar bisa zarginsu da yi wa jam’iyyar zagon-kasa.

Matasan Katsina sun yi zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga inda suke rufe babban hanyar zuwa Maradi na Nijar.

Hukumar Tarayyar Turai ta dakatar da rarraba takunkuman rufe fuska na China

Jirgin yaki mafi tsada mallakar sojojin Amurka ya fado a Florida ta Amurka.

Faransa ta kama daya daga cikin mutanen da suka haddasa kisan kiyashin Rwanda a 1994.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button