Tsaro

Cikin Daren Nan ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina.

Spread the love

Katsina Ta Dauki Zafi Cikin Daren Nan…

Daga Ahmed T. Adam Bagas

A cikin Daren nan ‘yan bindiga sun Kai Hari a Mai Daura dake yankin Karamar hukumar Faskari.

Ko a daren jiya Laraba ma ‘Yan Bindiga bisa babura sama da 100 sai da suka kai tagwayen hare-hare a kauyukan Kanawa da Kauyen Kanga dake cikin karamar hukumar DanMusa, inda Suka Kashe Mutane Takwas Da Jami’in Dan Sanda Daya, tare da jikkata wasu da dama.

Sai dai a nata bangaren rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta bakin Mai magana da yawun rundunar SP Gambo Isa ya tabbatar da kai hare-hare a jiya. Inda ya ce Mutum shidda aka kashe a harin na jiya.

Gambo Isa ya kara da cewa a lokacin da muke kokarin kai masu dauki, ashe barayin sun yi mana kwantan bauna, har jami’in mu guda ya rasa ransa.

Kuma yanzu haka kwamishinan yan sanda na jihar Katsina, Sanusi Buba ya bada umurnin tura karin jami’an tsaro na kwantar da tarzoma. Kuma an tura har da Mukkaddashin kwamishinan.

Allah Ya kawo mana Zaman Lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button