Labarai

Cikin Hanzari: Buhari yana ganawar gaggawa da Obasanjo, Yakubu Gowon, da sauran tsoffin shugabanni da Hafsoshin Tsaro.

Spread the love

SHUGABA Muhammadu Buhari a yanzu haka yana wata ganawa ta gaggawa da tsofaffin Shugabannin kasa, da Shugabannin tsaro.

Taron ba-zato, da Shugaban kasa ya kira, ba zai rasa nasaba da tashin hankali da halin tsaro da ake ciki a kasar ba, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama da kuma asarar dukiyoyi.

An fara taron ne da misalin karfe 10 na safe, amma ba a bayyana jadawalin ba.

Tsoffin shugabannin da ke halartar taron sun hada da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Janar Yakubu Gowon, Abdulsalam Abubakar (mai ritaya); tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Cif Ernest Shonekan.

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Gabriel Olanisakin; Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu; Darakta-Janar na Ma’aikatar cikin gida, Yusuf Bichi; da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ahmed Rufa’i.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button