Cikin lumana Gwamna Matawalle ya kuɓutar da mutane 11 da aka yi garkuwa da su ba tare da kuɗin fansa ba.
Jami’an gwamnatin Zamfara sun kubutar da mutane 11 da aka sace a daren ranar Asabar daga hannun wadanda suka sace su, sanarwar da Jamilu Iliyasu, Sakataren yada labarai na Gwamna Bello Matawalle ya fitar.
Iliyasu ya ce sakin mutanen ba tare da wani sharadi ba, wadanda suka fito daga karamar hukumar Bukkuyum ta jihar, sun bi hanyar ‘karas da sanda’ da Matawalle ya fara.
‘Karas da sanda’ kwatanci ne na amfani da haɗin lada da ukuba don haifar da halaye da ake so.
Iliyasu ya bayyana cewa jami’an gwamnati sun fara tattaunawa da ‘yan fashin nan take suka samu kiran gaggawa cewa an sace mutanen.
Ya ruwaito gwamnan yana cewa yarjejeniyar zaman lafiya ita ce hanyar da ta fi dacewa ga ‘yan fashi a jihar saboda ana samun zaman lafiya a hankali yayin da ake sakin wadanda aka sace ba tare da wani fansa ko wani sharadi ba.
Gwamnan wanda ya roki ‘yan bindiga da ba su tuba ba a jihar da su mika makamansu kuma su zama’ yan kasa na gari, duk da haka, ya gargadi wadanda suka ki yarda da zaman lafiya za su gamu da fushin doka matukar an kama su.
Yayin gabatar da wadanda aka sacen ga gwamnan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Alhaji Abubakar Dauran, ya nanata cewa da yawa daga cikin ‘yan ta’addan yanzu suna tuba daga munanan hanyoyinsu kuma sun amince da yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu da gwamnan ya gabatar.
Dauran ya bayar da tabbacin cewa ma’aikatar sa za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da jami’an tsaro domin samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.
Ya ce wadanda abin ya rutsa da su za a duba lafiyarsu a cibiyar gwamnatin jihar bayan haka za su sake haduwa da ‘yan uwansu.
Wadanda aka sace, maza 10, da mace daya, sun gode wa gwamnan kan samar musu da ‘yanci.