Tsaro
Cikin Watanni 6 Da Suka Gabata, Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama Da Dubu 1 Binciken Kungiyar Kare Hakkin Dil’adama Ta Amnesty International
Rahoton kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty international ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Yuni na 2020, Mutane 1’126 ne ‘yan Bindiga suka kashe.
Inda lamarin yafi shafa shine kudancin Kaduna inda ake tsammanin ‘yan Bindigar sun kashe mutane 366. Kungiyar ta fitar da bayanin hakane a rahoton da shugabanta, Osai Ojigho ya sakawa hannu.
Mun fahimci sauran jihohin da aka samu karin rikice-rikice sune Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara dadai sauransu.
Wasu mazauna yankunan da aka tattauna dasu sun bayyana cewa koda an gayawa jami’an tsaro basa zuwa akan lokaci sai bayan maharan sun tsere.
Mun ruwaito muku cewa Amnesty international ta bukaci gwamnati ta binciki wannan lamari.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe