Labarai

Cin Amana Da Kuntatawar Da Gwamnatin APC ke Mana, Tura Takai Bango~ Al’ummar Najeriya.

Spread the love

‘Yan Najeriya da dama sun fara fusata sakamakon tsadar rayuwa da suke ganin sakacin gwamnati ne ta kaisu ga haka.

suna kokawa da yadda farashin man fetur da wutar lantarki ke karuwa.

Tuni dai farashin kayan masarufi, irin su shinkafa da masara suka yi tashin-gwauron zabi a kasar.

Ita ma ƙkungiyar ƙkwadagon ƙkasar ta nuna rashin jin dadinta game da wannan lamari, har ta fara tunanin daukar mataki.

Yayin da wasu ma`aikata ke kukan ana zaftare masu albashin nasu, wasu kuma aikin ne suka rasa, sakamakon annobar Corona Virus.

Ana haka sai ga hukumar wutar lantarki ta yi ƙkarin kudin wuta da kusan ninkin farashinta na baya, kuma ko numfasawa `yan kasar ba su yi ba sai farashin litar man fetur ya tashi daga naira 148 zuwa dari 151.65.

Kungiyar daillalan man cewa ta yi, idan ba ta sayar da lita a naira 162 ba za ta kwana ciki.

Sai ko a Jiya Laraba Jam’iyyar Adawa ta PDP a Kasar tayi Ikirarin bata amince da Sabon Farashin Man Ba, Inda Tace Rashin Adalci da Kokarin jefa ‘yan Kasar cikin rikici da mawuyaci hali ne da gwamnatin APC da Shugaba Buhari ke kokarin jefa Kasar Nan In PDP.

A yau alhamis Ma Kungiyar daliban Jami’a a Jihar Ondo tayi Kira ga Shugaba Buhari da yayi Murabus, sakamakon Karin Kudin Wutar lantarki da man Fetur.

Sai dai wasu ‘yan Kasar sun zargi ‘Yan kasuwa ne da Alhakin hauhawar Kayan Masarufi, Wasu kuma Sunce Tsadar Abincin ba laifin Gwamnati bane Jarabawa ce kawai daga Allah.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button