Labarai

Cire Tallafi: Majalissar Wakilai ta bukaci a sake duba albashin ‘yan majalisa da alawus-alawus.

Spread the love

‘Yan majalisar wakilai na neman a sake duba albashinsu da alawus-alawus, bayan cire tallafin man fetur da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya tattaro cewa bukatar ta biyo bayan ganawar da ‘yan majalisar suka yi a ranar 11 ga watan Yuli bayan sun shiga wani zama na zartarwa a zaman majalisar.

NAN ta ruwaito cewa korafe-korafen da ‘yan majalisar ke samu daga albashi da alawus-alawus ne ya tilastawa majalisar shiga zaman zartarwa domin tada zaune tsaye.

‘Yan majalisar sun kuma kokawa shugaban majalisar, Tajudeen Abass game da jinkirin biyansu albashi da alawus-alawus, lamarin da ya sa wasun su shiga rance.

Sai dai daya daga cikin ‘yan majalisar da ya halarci taron amma ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar yin magana kan sakamakon zaman majalisar zartarwa ba, ya yi watsi da jita-jitar.

Da yake karyata rade-radin, dan majalisar ya ce kawai sun shaida wa shugaban majalisar cewa albashi da alawus-alawus din su ba za su iya biyan bukatar aikinsu ba, don haka ya zama dole a sake duba lamarin.

“Don haka babu wanda ya yi magana game da wani kudi ko an biya mu ko a’a,” dan majalisar ya bayyana.
Majiyar ta ce bukatar tasu ta biyo baya ne a halin da ake ciki a halin yanzu na tattalin arziki bayan cire tallafin da ya janyo wahalhalu, lamarin da ya sa kayayyaki da ayyuka suka yi tashin gwauron zabi a kasar.

Dan majalisar ya ce shugaban majalisar bai yi musu alkawarin komai ba game da sake duba albashi da alawus-alawus din su, domin irin wannan bukata ba za a iya biyan su ba sai bayan an bi tsari.

A cewar dan majalisar, kakakin majalisar ya shaida wa takwarorinsa cewa ba a cikin kasafin kudin shekarar 2023 ba a biyan su albashi da alawus-alawus.

A cewar majiyar, shugaban majalisar ba zai iya yin alkawarin komai ba, kuma “duk mun san halin da kasar ke ciki, dukkanmu muna fuskantar matsala iri daya”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button