Labarai

Cire tallafin man fetur: Ina jin zafin da kuke ji, ku yi sadaukarwa kadan – Tinubu ya roki ‘yan Najeriya

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu ya amince cewa cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan ya jawo wa al’umma wahala.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar Dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya a ranar Litinin, inda ya ce duk da cewa yana jin zafin da talakawa suke ji, amma akwai bukatar su kara sadaukarwa domin ci gaban kasa baki daya.

A cewar shugaban, rashin jin dadi na dan lokaci sakamakon cire tallafin ya zama dole don ceto kasar daga shiga cikin mawuyacin hali.

Ya ce, “Ina jin zafin da kuke ciki. Wannan wata shawara ce guda daya da ya kamata mu dauka domin ceto kasarmu daga shiga ciki da kuma kwace albarkatunmu daga kangin wasu tsiraru marasa kishin kasa.

“Na yarda cewa shawarar za ta dora wani nauyi a kan talakawan mutanenmu. Abin takaici, na roke ku ’yan uwana, ku kara sadaukarwa kadan don ci gaban kasarmu”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button