Civid-19:- Gwamnatin Jahar Neja ta Tsawaita dokar Hana Zirga Zirga sannan ta Sassauta….
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Neja Abubakar Sani Bello Lolo Na Neja ya Sanarda Karin Makonni 2 Na Takaita Zirga Zirga a Fadin Jahar A Kokarinsu Na Dakile Yaduwar Cutar Corona Virus a Jahar.
A daya Bangaren kuma Ya Sassautawa Al’ummar Jahar Inda Zasu Iya Fita Kwanaki 3 A Kowanne moko Domin Neman Abinda Za’asa A bakin Salati amma Da Sharadin Kowa zai sa Takunkumin Fuska (Face Mask) sanya Takunkumin Dole ne Ga kowanne Dan Jahar Duk Wanda Bai Sanya ba Zai Fuskanci Hukunci Inji Shi.
Ranakun Dai Za’a Fita Ranakun Talata, Juma’a da Lahadi daga 7:00 Na Safe Zuwa 12:00 Na Daren Kowacce Ranar.
Gwamnan ya ce `yan Adai dai ta Sahu ( KEKE NAPEP) Mutun Daya 1Tak zai Dauka a Bayan Mashin Disa San nan Ya tabbatar Ya sanya (Face Mask) da shi da Fasinjan.
Gwamnan yace Nan bada Dadewa ba Za’a Maida Almajiran Jahar Garinsu Na Asali Daga Jahar Nejan.