Civid-19: Gwamnatin Neja Ta Maida Trela Da Fasinja Sama Da 50 Legas…..
Ahmed T. Adam Bagas
A yau ne Wata babbar mota Trela da Ta taso daga Legas zuwa Kano Ta Iso Jahar Neja Gwamnatin Jahar ta Tilastasu Komawa Inda Suka fito.
Matafiyan Dai sun kai 50 a Cikin Trela Sannan Sun Rufa Tampol A Sama Wasu kuma Suna Saman Tampol Din, Da Jami’an Tsaron Suka Tsare so Sukace Gwamnatin Jahar ta Haramta wa Matafiya Bi ta Cikin Jahar. Idan kuma ba Hakaba za’a killace Fasinja har Na Tsawon Makonni 2.
Har Takai ga Jami’an tsaron Suka hada Dreban Trelar da Sakataren Gwamnatin Jahar Ahmed Ibrahim Matane ta waya, Matane yazo Wajen Motar Anan Gidan Kwana Kusa da Minna Sakataren Yace Yazama Dole matafiyan Su koma Legas Inda Suka Fito.
Domin Gwamnatin Ta sanya Dokar ta Baci a Jahar. Matane yace Babu wata mota da zatabi ta Jahar Idan ba Man Fetir ko Abinci ya dauko ba.