Lafiya

Corona Virus:- Giya Ta Kashe Mutane 600 A Kasar Iran.

Spread the love

Ahmed T. Adam Bagas

Ma’aikatar Kasar Iran Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane Dari 600 Da Suka Mutu Sakamakon Shan Barasa A Matsayi Kariya ko Rigakafin Cutar Covid-19 a Kasar.
Kasar Iran dai Tana Daya Daga cikin kashen da Corona tayi Ta Adi Sosai bayan Kasar Sin.

A Kwanakin Bayane dai Akayita Rubuce Rubuce a Shafukan Sada Zumunta Na Kasar Cewa Shan Giya yana Riga kafin Kamuwa da Cutar Nan Ta Corona Virus Kuma Da Dama Al’ummar kasar Suka Raja’a Kan Wannan Suka Rika Amfani da Giya Duk da Kasar Ta Haramta Shan Barasar Hakan Yasa Mutane 600 Suka Mutu Mutane 3,000 Sukayi Fama da Rashin Lafiya Sanadiyar Shan Giyar.

Jami’in Hulda da Jama’a Na Ma’aikatar Shara’ar Kasar Ne Ya fidda wannan Sanarwar.

Kasar Iran Din dai Tayi Famada wannan Cutar ta Numfashi Covid-19 Inda Tayi Sanadiyar Mutuwar Mutane Fiye da 4,000 Kuma Fiye da Dubu 62,000 Suna Dauke da Wannan Cutar.

Muna Fatan Allah ya Kawo mana Karshen Corona Virus A Duniya Baki Daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button