Uncategorized

CoronaVirus:- Gwamnatin Jahar Neja Ta Sanya Dokar Ta6aci Na Tsawon Makonni 2 a Jahar………

Spread the love

.

Ahmed T. Adam Bagas

Gwamnan Jahar Neja, Abubakar Sani Bello Lolo Yace Ya sanya Dokar Tabaci a Jahar Kasancewar An Samu Mutun Na Farko da Yakamu da Cutar A Jahar.

Gwamna Abubakar din Yace Ansa Dokar ne Kasancewar An Samu Wani Dan Anguwar Limawa dake Cikin Kwaryar Minna Da Ya taho Daga Legas Yana Dauke da Cutar Ta Corona Virus Kuma Yayi mu’amala da Mutane Da Dama a Anguwar Tasu, Hakan Yasa Gwamnan ya Umarci Ma’aikatan Lafiya da Killace Anguwar Ta Limawa Har Tsawon Makonni 2 Domin Gudun Yaduwar Cutar.

Sai Dai Gwamnan Yace Baza’a Gudanar da Sallar Juma’a Ko Bauta A Majami’u Ba Ko kuma Taron Al’umma ba, Sai dai Gwamnan yace Ranar Alhamis 16 ga Wannan watan da Ranar Litinin 20 ga wata Jama’a Su Fita Domin Neman Abinda Zasuci daga 6 Na Safe zuwa 6 Na Yamma.

Gwamnan Yace Ya zama Dole Kowa Yabi Umarnin Gwamnati, Duk Wanda Ya Karya Doka Doka Zatabi Ta Kanshi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button