Lafiya
CoronaVirus:- Hukumar Da Ke Yaki Da Cutar Numfashi Ta Covid-19 Ta Kaddamar Da Feshi A Abuja.
Tareda Wakilin Jaridar Mikiya~Ahmed T. Adam Bagas
A Yau Litinin ne Dai Hukumar Yakida Corona Virus Ta Nigeria NCDC Ta Kaddamar da Feshin Rigakafin Cutar a Titunan Birnin Tarayya Abuja.
Idan Baku mantaba Tun Bayan Bullar Cutar A kasar Nan Mahukunta Basu Tsaya ba Suna Ta Fadi Tashi Don Ganin Andakile Yaduwar Cutar a Fadin Kasar Baki daya. Kawo Yanzu Dai Cutar Ta Corona Tayi sanadiyar Mutuwar Mutane 5 An samu Mutane 210 da Suke Dauke da Cutar A Fadin Kasar Nan.