Labarai

Covid-19: A Jigawa An Sami Tabbacin Mutuwar Mutum Daya, An Kuma Kara Dokar Hana Zirga-Zirga A Wasu Wuraren.

Spread the love

Daga Haidar H Hasheem Kano

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban hukumar lafiya ta jahar Jigawa Dk Abba Zakari, inda ya tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikin masu dauke da cutar ta corono virus.

Dk Abba Zakari yace yanzu adadin wadanda ke dauke da cutar a fadin jahar yazama mutum tara, inda kai tsaye za’a kara fadada kullen zaman gida a wasu sassan jahar domin kaucewa yaduwar cutar.

Cikin garuruwan da dokar zata shafa sun hada da Dutse, Gwaram, Miga, Auyo inda tuni dama an sanya dokar hana zirga zirga a Kazaure, Birinin Kudu, Gujungu wacce take karamar hukumar Gumel a jahar.

Cikin jawabin da ya gabatar a yau a Dutsen babban birnin jahar Jigawa yace Gwamnati tana shirin fadada gurin gwajin masu dauke da kwayar cutar ta corona virus zuwa wajajen gwaji masu zaman kansu, inda hukumar lafiya ta NCDC ta amince dasu.

Yayin gabatar da jawabin nasa ya baiyana cewa sabuwar dokar da aka sanya a wasu sassan jahar zasu fara aikine a daren ranar Juma’a mai zuwa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button