Adadin wadanda suka kamu da coronavirus a Najeriya ya karu zuwa 305 bayan wasu 17 sun harbu a jiya Juma’a, a cewar hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka.
Daga cikinsu, takwas a Jihar Legas suke – wadda yanzu take da 163 kuma mafi yawa a kasar.
Jihohin da aka samu sababbin wadanda suka kamu da Cutar Kamar Haka:-
Lagos – 8
Katsina – 3
Abuja – 2
Neja – 1
Kaduna – 1
Anambra – 1
Ondo – 1
Allah Ya Kawo mana Karshen Wannan Masifar.
Ahmed T. Adam Bagas