Covid-19: Anyi Sallar Juma’a A Wani Masallaci A Kano….
Daga Ahmed T. Adam Bagas
A Jiya Alhamis ne dai Gwamnan Jahar Kano Dr. Abduullahi Umar Ganduje ya bada sanarwar sanya dokar Tabaci Har Na tsawon Kwanaki 7 domin gudun yaduwar Corona Virus a Jahar.
Dokar ta Kunshi Hana zirga zirga, da kowanne Irin Taron mutane da Sallar Jam’i da Zuwa Choci da sallar Juma’a.
Duk da wannan Dokar An gudanar da Sallar Juma’a A Wani masallaci da ake kira Masallacin Isah Kafinta Dake Gwammaja a Karamar Hukumar Dala dake Cikin Kwaryar Birnin Kano.
Rahoto ya tabbatar da Anyi Sallar Masallacin Ya cika kamar yadda Akasaba yi a baya, sai dai Anga Jami’an Tsaro Sun Iso Masallacin Ana Tsammanin Limamin Za’a Kama, sai dai Kawo yanzu bamuda Labarin Abinda ya kawo Jami’an Tsaron.
Ku kasance da Jaridar Mikiya Domin Jin Yadda Ta Kaya.