Labarai

COVID-19 El Rufa’i zai sake Saka Dokar kulle a jihar kaduna.

Spread the love

Gwamna Nasir El-rufai, ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a cikin jihar sa sannan ya yi barazanar sanya sake Dokar kulle a cikin jihar baki daya idan har adadin masu kamuwa da cutar ya ci gaba da karuwa.

El-Rufai ya ce ya damu matuka cewa yawan adadin masu kamuwa da cutar nan ba da jimawa ba zai mamaye tsarin kiwon lafiyar jihar idan ba a yi wani abu cikin gaggawa don hana yaduwar kwayar ba.

Ya zuwa yanzu jihar Kaduna ta samu kaso 30 cikin 100 na sabbin masu kamuwa da cutar ta COVID-19 kowace rana a cikin watanni biyu da suka gabata.
Gwamnan ya koka kan yadda wasu mazauna yankin suka ki bin duk matakan tsaron da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tanada.

Ya yi ishara da cewa idan halin yanzu ya ci gaba, akwai yiwuwar sake kulle nan ba da daɗewa ba.

Gwamnan ya bayar da umarnin cewa dole ne dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar su yi gwajin COVID-19 a matsayin wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar a jihar.
Gabanin bukukuwan Kirsimeti, Gwamnan ya gargadi mazauna garin da su yi taka-tsantsan, ta hanyar kaurace wa manyan taruka, Kuma a sanya facemask a koyaushe, da kuma bin wasu matakan tsaro da za su hana su kamuwa da COVID-19

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button