Lafiya
Covid-19: Gwamnan Sokoto Ya Ruga Wajen Shugaban Kasa Neman Dauki…
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Sokoto Hon. Aminu Waziri Tambuwal Ya Garzaya Birnin Tarayya Abuja Wajen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Domin Neman Agajin Gaggawa kan Cutar CoronaVirus a Jahar.
Kawo Yanzu dai Cutar Ta Kama Mutane 66 Ta Kashe 8 A Jahar Ta Sokoto, Hakan Yasa Tambuwal Din Ya Garzaya Wajen Shugaban Kasa domin Neman Dauki.
Allah Ya Kawo mana karshen Wannan Masifar.