
Daga Ahmed T. Adam Bagas
Gwamnan Jahar Neja Abubakar Sani Bello Lolo ya Bada Umarnin Ayi Feshin Kashe Kwayoyin Cutar Corona Virus a Gidajen Yari a Jahar.
Lolo ya Dauki wannan Matakin ne A kokarinsa Na Dakile yaduwar Cutar a Tsakanin Fursunonin dake Zaman Kaso a gidajen Yarin.
Lolon ya Umarci Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jahar NISEPA da ta Kaggauta Tsaftace Gidajen Yarin kuma ayi Feshin Rigakafin Yaduwar Cutar a gidajen Yarin, ganin Yadda Cutar ke karuwa a Kasar Nan.
Kawo Yanzu dai An yi Feshin a gidajen Yarin Minna Babban Birnin Jahar da Kuma na Karamar Hukumar Bidda, Saura Na Kontagora da Sauransu.
Kawo yanzu dai Mutane 66 ne ke Dauke da Cutar a Fadin Jahar Neja Inji;- Hukumar Kulada Cututtuka Masu Yaduwa ta Kasa NCDC.