Labarai
COVID-19: Haryanzu bamu Tabbatar za’a koma Makarantu a Ranar 18 ba muna Kan Sake dubawa ~Inji Ministan Ilimin Adamu Adamu.
Gwamnatin Tarayya a ranar Litinin ta ce haryanzu Bata Tabbatar da za’a koma Makarantu ba a ranar 18 ga watan Janairun da aka kayyade domin sake komawa makarantu a duk fadin Najeriya.
Ta danganta lamarin ne da matsin lambar cutar COVID-19 Karo na biyu da kasar ke fuskanta.
Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyi a yayin ganawa da manema labarai da rundunar ‘yan Kwamitin ta shugaban kasa suka yi kan COVID-19 a Abuja.
Ministan ya ce, “A ranar 18 ga watan Janairu da za a sake dawowa, muna kan sake duba faruwar hakan Zamu sake duba shi. Inji Minisatan.